Monday, July 13, 2009

Sabon Kitso. A Hausa Poem on the purported Nigerian Rebranding

SABON KITSO (for those trying to rebrand)
Sabon kitso
Sabon kitso
Tsalle da nitso
a sabon kitso
Ba su tunawa?
Ba a Sabon Kitso
Da kwarkata
Ba juyi, ba rawa
Ga gashi ta yi kawa
Da kwarkwata
Mun yaudara
Muna takama da kabido
Hadarin kuma- na kasa

Sabon kitso!
Gashi a cinye-
Gaba da baya
Mai kitson mu kuma-
Kuturuwa!
Kuturuwa mai-kitson makauniya
Makafi!
Ana yaudaran ‘ya’yan mu
Gurbin ido ba ido bane
Nemi gurbin:
Idon zai fado ciki
Wanke gashi:
Ba sai an yi sabon kitso ba
Kori kuturuwa da tsabta
Ba da kidi da rawa
kare zai san ana biki ba
A gani a kasa
kare ya ce,
A gani a kasa!